Shugaba Buhari zai halarci taron rantsar da sabon Shugaban kasar Liberiya

Shugaba Buhari zai halarci taron rantsar da sabon Shugaban kasar Liberiya

- Za a rantsar da sabon Shugaban kasa Liberia wannan makon

- Kasashen Duniya har da Najeriya za su je wajen wannan biki

- Ana sa rai har Kasar Amurka ta aika tawaga zuwa Monrovia

Mun samu labari cewa Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari yana cikin wadanda za su halarci taron rantsar da sabon Shugaban kasar Liberiya George Weah a karshen makon nan. Har Kasar Amurka za ta tura Tawaga wajen nadin kasar.

Shugaba Buhari zai halarci taron rantsar da sabon Shugaban kasar Liberiya

Shugaba Buhari zai wajen nadin sabon shugaba Weah

Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya ne zuwa kasar ta Afrika a Ranar Lahadi ya hadu da wasu Shugabannin Nahiyar. Wani babban jami’in Kasar ta Liberiya Jarvis Witherspoon ke bayyana hakan a Garin Monrovia a jiya Alhamis dinnan.

KU KARANTA: Ban ce ba zan yi takara ba Inji Shugaba Buhari

Witherspoon ya bayyanawa Duniya cewa Shugaba Buhari na Najeriya da sauran shugabannin Kasashe irin su Guinea, Sierra Leone, Cote D’Ivoire, Cape Verde, Afrika ta Kudu, Gabon, Guinea, Ghana, da Togo su na cikin wadanda za su halarci taron.

Sauran Kasashe irin su Masar da Faransa za su tura Jakada yayin da Sanagal ma za ta aika wakilin ta a wajen. Za a rantsar da tsohon ‘Dan kwallon ne a matsayin sabon Shugaban kasa a filin wasa na Samuel Kanyon Doe da ke Birnin Monrovia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel