Sanata Shehu Sani ya caccaki jam'iyyarsa ta APC, PDPn ma bai barta ba

Sanata Shehu Sani ya caccaki jam'iyyarsa ta APC, PDPn ma bai barta ba

- Sanata Shehu Sani yayi kaurin suna wajen caccakar APC da PDP da ma masu mulki tun zamanin sojoji

- BAsu ga-maciji da gwamnan jiharsa NAsir El-Rufai

- YA ce APC bata da liba, PDP kuma kunya ta ishe ta

Sanata Shehu Sani ya caccaki jam'iyyarsa ta APC, PDPn ma bai barta ba

Sanata Shehu Sani ya caccaki jam'iyyarsa ta APC, PDPn ma bai barta ba

Sanata na Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce jam'iyyarsa ta APC ta rasa alkibla, inda ta kasa tsayar da muhimmin ra'ayi ko daya, a cewarsa ma dai jam'iyyar bata da juriya, inda yace bata da banbanci ma da jam'iyyar adawa ta PDP.

Ya kuma kara da cewa, ita ma PDP bata da wata madogara kuma bata da fuskar kallo talakka, musamman irin badakalar da ta tafka a zamanin mulkin ta, wanda a yanzu ta ffito fili, cewa barayi sun washe dukiyar kasa.

DUBA WANNAN: Fadar Aso Rock ta karyata batun kin takarar Buhari

Sanatan, yace maimakon shuwagabanni da aka zabo su yi wa jama'a aiki, sai suka bige da kamffe na 2019 tun basu iyar da aikinsu ba na wannan zango, inda yayi tir da wadannan halaye.

Shi dai Sanatan, a yadda jama'a ke hasashe, yana shinshinar takarar kujerar gwamnan Kaduna ne a jam'iyyarsa ta APC ko kuma a wata jam'iyyar, muddin ya sha kaye a hannun gwamnansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel