Jihohi hudu sun baiwa gwamnatin tarayya goyon bayan haƙo man fetur a Arewa

Jihohi hudu sun baiwa gwamnatin tarayya goyon bayan haƙo man fetur a Arewa

Gwamnonin jihohin Sakkwato, Kebbi, Zamfara da kuma Katsina, sun yi shirin haɗa gwiwa tare da gwamnatin tarayya domin tallafawa wajen haƙo man fetur da ma'adanansa a yankin nasu na Arewa maso Yamma.

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, shine ya bayyana hakan da cewar, gwamnatinsa za tayi hoɓɓasa wajen goyon bayan gwamnatin tarayya domin samun nasarar gudanar da haƙo man fetur a kwarirrikan jihar tasa.

Aminu Waziri Tambuwal

Aminu Waziri Tambuwal

Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, a yayin wani taro na lacca da aka gudanar akan haƙe-haƙen man fetur da ma'adanansa a jami'ar Usman Danfodio dake jihar ta Sakkwato.

KARANTA KUMA: Kotu ta yanke wa shugaban ƙungiyar haɗin kan malaman musulunci hukuncin ɗaurin rai da rai

Gwamnan yake cewa, a sakamakon kididdigar bincike da wani kamfanin kasar Sin ya gudanar karkashin gudunmuwar gwamnatin jihar sa, ya tabbatar da cewa akwai yalwar man fetur da ma'adanansa a cikin kasar ta Sakkwato.

Ya kara da cewa, Najeriya tana bukatar yalwar man fetur da ma'adanansa domin ci gabanta da kuma haɓakar tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel