Wani babba a APC ya ba Shugaban kasa Buhari shawara ta musamman

Wani babba a APC ya ba Shugaban kasa Buhari shawara ta musamman

- Wani babba a APC yace akwai matsala a cikin Jam’iyyar mai mulki

- Kpodo ya zargi Shugaba John O. Oyegun da rashin hada kan kowa

- Jigon na APC yayi kira ga Shugaba Buhari da kuma Jam’iyyar kasar

Wani babba a cikin Jam’iyyar APC Cif Richard Perekeme Kpodo yayi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rika tuntuben barin Jihohi domin zaben wadanda za a ba mukamai a Kasar domin a rika tafiya da kowa a Jam'iyyar.

Wani babba a APC ya ba Shugaban kasa Buhari shawara ta musamman

Richard Perekeme Kpodo yace akwai matsala a APC

Bayan maganar nade-nadi inda aka yi tuntuben nada har da matattu kwanakin baya, Richard Perekeme Kpodo ya kuma yabawa Shugaban kasar na nada Minista Rotimi Amaechi a matsayin wanda zai jagoranci yakin nemen zaben sa a 2019.

KU KARANTA: An hurowa Shugabannin Jam'iyyar APC wuta

Perekeme Kpodo ya bayyanawa Legit.ng cewa akwai matsala a Jam’iyyar inda ake samu rashin tafiya tare tsakanin Shugabannin Jam’iyyar da ke sama da kuma bangaren Jihohi. Ya daura laifin ne kan Shugaban Jam’iyyar John Odigie Oyegun.

Babban ‘Dan Jam’iyyar a Jihar Bayelsa ya koka da irin rashin hadin kan da ake samu ya nuna cewa akwai wadanda an sallame su daga Jam'iyyar a Jihohin su amma har yanzu ana damawa da su a Gwamnatin wanda hakan bai dace ba a tafiyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel