Mulki sai da lissafi, don haka ba’a raba ni da Kalkuleta – Inji Gwamnan jihar Jigawa

Mulki sai da lissafi, don haka ba’a raba ni da Kalkuleta – Inji Gwamnan jihar Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru ya bayyana cewa tafiyar da mulki sai da lissafi, don haka ne ya sanya ba’a raba shi da na’urar lissafi, wato Kalkuleta, hakan ya sanya ake kiransa da suna Baba mai Kalkuleta.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa, inda ya bayyan cewa sau dayawa za’a kawo masa bukatar yin abu ta wani hanya, amma idan ya auna, sai ya ga cewar za’a a fi samun sakamako mai kyau idan aka bi ta wata hanyar daban.

KU KARANTA: Buhari ya lashi takobin ladabtar da duk masu shirin tayar da zauni tsaye a 2019

A cewar Gwamnan, don haka idan ya bada shawara aka bi, cikin ikon Allah sai kaga an samu biyan bukata ba tare da kashe makudan kudade ba.

Mulki sai da lissafi, don haka ba’a raba ni da Kalkuleta – Inji Gwamnan jihar Jigawa

Badaru

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan yana fadin duk abinda mutum zai yi sai da lissafi matukar nasara ake nema, inda ya kara da cewa lissafin da yake yi ya sanya jihar bata shiga rudanin rashin biyan albashi na watanni biyar ba shekarar 2016, kamar yadda wasu jihohin suka shiga.

Da aka tambayeshi ko da gaske yana da Kalkuleta, sai yace yana dasu har guda biyu a Ofis, don kuwa ba’a raba shi da Kalkuleta, rayuwa sai da lissafi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel