An sake yin garkuwa da wasu mutane farar fata a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

An sake yin garkuwa da wasu mutane farar fata a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Labarin da muke samu mai sosa zuciya yanzu haka daga majiyar mu shine wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun sake sacewa tare da yin garkuwa da wasu farar fata 'yan kasar waje.

Kamar dai yadda muka samu, majiyar ta mu ta tabbatar da cewa an sace mutanen ne a kan hanyar nan ta Abuja zuwa Kaduna bayan sun samu nasarar kashe dan sandan dake yi masu rakiya a daren jiya Alhamis.

An sake yin garkuwa da wasu mutane farar fata a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

An sake yin garkuwa da wasu mutane farar fata a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Legit.ng dai ta samu cewa lamarin dai ya faru ne a dai-dai garin nan na Kagarko, wata karamar hukumar jihar Kaduda.

A wani labarin kuma, Kotun daukaka kara dake zaman ta a garin Abuja, babban birnin tarayya a jiya ta tsayar da ranar 15 ga watan Maris mai kamawa a matsayin ranar da zata fara sauraren karar da wani soja da aka kora mai suna Manjo Janar Ibrahim Sani ya shigar a gabanta yana kalubalantar hukuncin.

A baya dai cikin wata Yulin da ya gabata ne dai wasu manyan sojoji da suka hada da Laftanal Janar Tukur Buratai suka tabbatar da samun Manjo Janar ibrahim din da laifi dumu-dumu tare da karya wata dokar rundunar game da wani filin da ake zargin sa da tafkawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel