Rikicin makiyaya: Sarkin musulmi ya caccaki gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro

Rikicin makiyaya: Sarkin musulmi ya caccaki gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro

A ranar alhamis din da ta gabata ne, sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya caccaki gwamnatin tarayya tare da hukumomin tsaro na kasar nan dangane da kashe-kashen da makiyaya ke yi a fadin kasar musamman a jihohin Benuwe da Taraba.

Sultan din na Sakkwato ya kuma barrantar da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, daga duk wani laifi na kashe-kashen manoma a wasu sassan kasar nan da ake zargin makiyaya na Fulani da aikatawa.

Sarkin musulmi ya gabatar da wannan sanarwa ne bayan kwana guda da daruruwan 'yan asalin jihar Benuwe suka mamaye farfajiyar majalisar dokoki ta kasa dake Abuja, inda suka yi zanga-zangar rashin amincewa da umarnin gwamnatin tarayya a burtalan kiwon shanu.

Sarkin Musulmi; Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Sarkin Musulmi; Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Jaridar Vanguard ta ruwaito a ranar da ta gabata cewa, makiyaya sun harbe wata mai juna biyu har lahira a jihar Ekiti, bayan lokutan da basu wuci awanni 24 ba da gwamna Ayo Fayose ya gana da kungiyar Miyetti Allah, makiyaya da kuma mafarauta a jihar.

KARANTA KUMA: Badaƙalar N92m: Hukumar EFCC ta cafke ɗan tsohon gwamnan jihar Nasarawa

A yayin taron hadin kan addinai da aka gudanar a birnin na tarayya, Sultan ya bayyana damuwa dangane da yadda gwamnatin tarayya da kuma hukumomin tsaro suke nuna halin ko in kula da mallaka tare da yawo da makamai da makiyaya ke yi, duk da jerin hare-hare da ake kaiwa wasu sassa na kasar nan.

Ya kara jaddada cewa, kungiyar Miyetti Allah ba ta da ta cewa akan kowane bafulatani dake salwantar da rayuka al'umma ba tare da hakki ba, inda ya gargadi gwamnatin tarayya da kuma hukumomin tsaro da su tashi su farga akan wannan lamarin da ya riga da wuce gona da iri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel