Sule Lamido ya roki Bola Tinubu ya rabu da Buhari ya dawo Jam’iyyar PDP

Sule Lamido ya roki Bola Tinubu ya rabu da Buhari ya dawo Jam’iyyar PDP

- Sule Lamido ya nemi Bola Tinubu ya fice daga Jam’iyyar APC

- Tsohon Gwamnan yana ganin APC ba ta san darajar Tinubu ba

- Sule yace Shugaba Buhari da APC ba za su kai labari ba a 2019

Tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido kuma ‘Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP ya fadawa Bola Ahmed Tinubu cewa APC ba ta san amfanin sa ba don haka ya dawo PDP.

Sule Lamido ya roki Bola Tinubu ya rabu da Buhari ya dawo Jam’iyyar PDP

Sule yace ya kamata Tinubu ya rabu da Buhari

Sule Lamido ya bayyana cewa Jam’iyyar APC mai mulki ba ta san darajar Bola Tinubu ba don haka babu dalilin ya cigaba da zama a Jam’iyyar. Babban ‘Dan adawar ya nemi Tinubu ya tattara ya koma Jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Sule ya caccaki Gwamnatin APC ta Shugaba Buhari

Sule Lamido ya roki Bola Tinubu ya rabu da Buhari ya dawo Jam’iyyar PDP

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido yace Buhari zai fadi zabe

Tsohon Gwamnan dai yana ganin cewa Shugaba Buhari zai sha kashi a zaben 2019 sai dai yana ganin ana iya fuskantar matsala da zarar Buhari bai amince da sakamakon zaben shugaban kasar ba idan ya sha kayi.

Sule ya bayyana wannan ne duk a wajen wani taro da Jaridar Daily Trust ta shirya a makon nan. Tsohon Gwamnan na Jigawa yana ganin babu abin da ya rage a APC da zai sa Bola Tinubu ya cigaba da zama a Jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel