Kasar Yarbawa ba su yi na’am da tayin Shugaba Buhari kan rikicin Makiyaya ba

Kasar Yarbawa ba su yi na’am da tayin Shugaba Buhari kan rikicin Makiyaya ba

- Jihar Osun tace ba ta bukatar Gwamnatin Tarayya ta bude gandu

- Gwamnati na kokarin karbar filayen kiwo domin warewa Makiyaya

- Wasu Jihohi ba su yi naam da wannan tsarin ba saboda wasu dalilai

Yanzu haka Gwamnatin Tarayya ta ci karo da wata sabuwar matsala wajen shawo karshen rikicin Makiyaya bayan da wasu Jihohin su ka ki yin na’am da tayin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan na shawo karshen matsalar da ake fama da ita.

Kasar Yarbawa ba su yi na’am da tayin Shugaba Buhari kan rikicin Makiyaya ba

Aregbosola bai yarda ya warewa Gwamnatin Tarayya filin kiwo ba
Source: Depositphotos

Gwamnan Jihar Osun Rauf Aregbosola bai amince da kafa gandun kiwon dabbobi a Jihar sa ba. Gwamnan yace yanzu haka su na da hanyar da su ke bi na shawo karshen rikicin Makiyaya da mutanen Gari a Jihar don haka babu dalilin ware wani fili.

KU KARANTA: APC tana kokarin fara shirin lashe zaben 2019

Kwamishinan yada labarai na Jihar Adelani Baderinwa ya bayyanawa manema labarai wannan a jiya. Baderinwa yace tuni su ka kafa kwamiti da ke kula da duk wani Makiyayin da ya shiho Jihar domin yin kiwo don haka ba su fama da matsalar nan a Jihar.

Gwamnatin Tarayya na kokarin kafa gandun kiwon dabbobi a fadin kasar domin samun wuraren da Makiyaya za su rika kiwo ba tare da shiga gonakin jama’a ba. Sai dai wasu Jihohi irin Abiya da Taraba da sauran su na kukan cewa ba su da isasshen fili.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel