Kuma dai! Rundunar Sojin Najeriya na bukatar karin N18bn domin yaki da ta'addanci

Kuma dai! Rundunar Sojin Najeriya na bukatar karin N18bn domin yaki da ta'addanci

- Babban Hafsin Sojin Kasan Najeriya, Lafatant Janar Tukur Buratai ya yi kira ga Majalisar Dattawa ta dage takunkumin da ofishin shirya kasafin kudi na kasa ke amfani dashi

- Buratai kuma ya bukaci Majalisar ta kara wa Rundunar Sojin N18.177bn domin taimaka musu wajen magance kalubalen rashin tsaro da kasar ke fuskanta

- 'Yan Majalisar sun amince da bukatar ta sa na cire takunkumin da ofishin shirya kasafin kudi ta sanya wa Rundunar.

Shugaban Hafsin Sojin Kasan Najeriya, Laftanat JanarTukur Buratai ya nemi Majalisar Tarayyah ta kara adadin kudin ta aka ware wa Rundunar Sojin da naira biliyan 18.177 domin Rundunar ta samu daman yaki da ta'addanci da kuma sauran matsalolin tsaro da ke adabar kasar nan.

Kuma dai! Rundunar Sojin Najeriya na bukatar karin N18bn domin yaki da ta'addanci

Kuma dai! Rundunar Sojin Najeriya na bukatar karin N18bn domin yaki da ta'addanci

Buratai ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu a yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar domin kare kasafin kudin Rundunar tasa kamar yadda jaridar Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Kwana daya bayan taron sulhu a Ekiti, Makiyaya sun kashe wata mata mai ciki

Shugaban Rundunar Sojin kuma ya nemi a Yan Majalisar su cire takunkumin kudi da ofishin Shirya kasafin kudi na kasa ta sanya wa Rundunar. Ya ce takunkumin yana kawo cikas ga Rundunar wajen samin kudaden ta ta ke bukata domin sayan kayayakin yaki da kuma horas da jami'an rundunar.

Bayan sunyi la'akari da kalubalen da Rundunar Sojin ke fuskanta wajen yaki ta ta'addanci a kasar nan, Yan Majalisar sun amince da cewa akwai bukatar a kara sake wa Rundunar Sojin mara kan kasafin kudi, sun kuma amince da cire takunkumin da ofisin shirya kasafin kudin ta sanya wa Rundunar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel