Hadimin Gwamna Ortom ya zargi 'yan sanda da mara wa makiyaya baya

Hadimin Gwamna Ortom ya zargi 'yan sanda da mara wa makiyaya baya

- Hadimin Gwamna Ortom, Terver Akase ya zargi Rundunar Yan Sanda da aran bakin makiyaya da cin musu albasa

- Akase kuma ya zargi Kakakin Rundunar Yan Sandan ta rage adaddin mutanen da suka mutu a Jihar

- Ya kuma musanta zargin cewa Gwamna Ortom yana daukan nauyin yan bindiga a Jihar

Gwamnatin Jihar Benue ta yi zargin cewa Rundunar 'Yan Sandan Najeriya tana goyon bayan Makiyaya wanda gwamnatin ke zargin kai hare-hare a sassa da yawa na jihar. Ya fadi hakan ne yayin da yake mayar da martani ga kalaman kakakin rundunar yan sanda, Jimoh Moshood.

Hadimin Gwamna Ortom ya zargi 'yan sanda da mara wa Makiyaya baya

Hadimin Gwamna Ortom ya zargi 'yan sanda da mara wa Makiyaya baya

Babban Sakataren kafafen yadda labarai na Gwamnan Jihar Benuwe, Terver Akase ya kuma zargi Rundunar ta Yan Sanda da rage adadin al'ummar da suka rasa rayukansu a Jihar.

KU KARANTA: Sunyi garkuwa da wata yarinya yar shekaru 14, sun nemi N100m kudin fansa

A yayin da yake magana a wani shiri mai suna 'Sunrise' a gidan talabijin na Channels, Sakataren kafafen yadda labaran ya ce duk zuwan Sifeta Janar na yan sanda jihar da kuma baza jami'an tsaro a sassa daban-daban na Jihar, har yanzu ba'a dena kashe mutane ba.

Hadimin Gwamna Ortom kuma yayi raddi ga Kakakin Rundunar Yan Sanda Jimoh Moshood inda ya ce ba gaskiya ba ne cewa Gwamna Ortom ya na daukan nauyin yan bindiga a jihar, ya ce Gwamna Ortom mutum ne mai bin doka da oda, hakan ne ya sa ya yi ta kira ga shugaban kasa da sauran hukumomin tsaro su kawo masa dauki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel