Shugaba Buhari da sauran Shugabannin Kasashe da shekarun su ya ja

Shugaba Buhari da sauran Shugabannin Kasashe da shekarun su ya ja

- The Spectator Index tace Buhari yana cikin tsofaffin Shugabanni

- Donald J. Trump na Kasar Amurka ya haura shekaru 71 a Duniya

- Ba a kawo wasu Shugabannin da ba su shahara sosai ba a jerin

Bincike ya nuna mana Shugaba Buhari yana cikin fitattun Shugabannin Kasashe 5 na farko da shekarun su ya ja a Duniya. Shugaban na Najeriya dai ya cika shekaru 75 ne a karshen bara. Sarauniyar Ingila ba ta cikin lissafin.

Shugaba Buhari da sauran Shugabannin Kasashe da shekarun su ya ja

Shugaban Amurka Donald Amurka da Sarki Salman

Muhammadu Buhari ne na 4 a tsufa inda Sarki Salman na Saudiyya da ke da shekaru 82 sannan da kuma Shugaba Ali Khamenei na Iran mai shekaru 78 da Shugaba Micheal Temer na kasar Brazil ne kurum su ka sha gaban sa yanzu.

KU KARANTA: An haramta Kungiyar IPOB a Najeriya

Shugaba Buhari da sauran Shugabannin Kasashe da shekarun su ya ja

Shugaba Ali Khamenei na Kasar Iran mai shekara 78

The Spectator Index tace Donald Trump ne ke bayan Shugaban na Najeriya mai shekaru 71. Shugaban Israila Benjamin Netanyahu yana da shekaru 68 inda Modi na Indiya ya ke da shekaru 67. Vladimir Putin kuwa ya ba shekaru 65 baya.

A cikin jerin tsofaffin Shugabannin Kasashen akwai irin su Recap Erdogan, Angela Merkel, Theresa May da El Sisi na Masar wanda duk sun haura shekaru 60 a Duniya. Ba mu kawo wasu Shugabannin kasashen da ba su kai wadannan fice ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel