Ba mu san inda Okorocha ya dusa ba – In ji mazaunan Imo

Ba mu san inda Okorocha ya dusa ba – In ji mazaunan Imo

Al’ummar jihar Imo sun damu matuka game da rashin gwamnatin jihar ta bayyana ra’ayinta game da shirin kafa filayen kiwo shanu kamar yadda sauran gwamnatocin yankin suka yi.

Sakamakon rahotanni cewa gwamnatocin jihohi na Enugu da Abiya sun ki amince da shirin kebe filayen kiwo shanu ga makiyaya wanda gwamnatin tarayya ta fito da ita, ‘yan asalin jihar Imo sun yi zargin cewa gwamnan jihar, Rochas Okorocha, har yanzu bai furta komai a kan batun ba.

Wadansu da suka yi magana da majiyar Legit.ng a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu a Owerri, sun yi iƙirarin cewa shiru ta Okorocha game da batun kafa filayen kiwon shanu za a iya bayyana shi a matsayin amincewa da tsarin.

Wasu kuma sun bukaci gwamnan cewa ya kamata ya fito ya bayyana ra’ayinsa a kan batun kamar yadda sauran gwamnonin jihohi daga yankin kudu maso gabashin kasar suka yi.

Ba mu san inda Okorocha ya dusa ba – In ji mazaunan Imo

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha

Amma mutane da dama sun bayyana cewa ko Okorocha ya amince da shirin ko bai amince ba, cewa matsayin kungiyar dattawan ‘yan kabilar Igbo wato Ohanaeze Ndigbo shine zai zama mafi girma.

KU KARANTA: Rundunar soji ta tura jami’anta neman turawan da aka sace a Kaduna

A ra'ayinsa, tsohon shugaban kungiyar, Farfesa Chidi Osuagwu ya ce, "Ina tsammanin matsayin kungiyar ya rinjayi gwamnoni a kan wannan batu. Kungiyar Ohanaeze ta nuna cewa Igbo suna da masana'antun shanu wato ‘muduru cow industry’ a cikin yankin Igboland”.

"Kamar yadda yake da alaka da kiwon shanu, Igbo suna da masana'antun kiwon shanu wanda yakin basasa na Biafran ya rushe. Bayan yakin, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin za ta taimaka wajen sake farfado da masana'antar”.

"Yanzu da yake suna magana ne game da samar da filayen kiwon shanu a Najeriya, Igbo suna buƙatar cewa gwamnati ta goyi bayanmu don sake gina masana'antar wanda yakin basasa ta hallaka kuma gwamnatin tarayya ta yi alkawarin sake farfado da ita. Lokaci ya yi da za su cika alkawarin", in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel