An hurowa Shugabannin APC wuta su kira babban taro na kasa

An hurowa Shugabannin APC wuta su kira babban taro na kasa

- An nemi Jam'iyyar APC su kira babban taron gangami na kasa

- Kwanan nan Gwamnoni su ka watsawa Jam'iyyar kasa a ido

- Wa'adin Shugabannin Jam'iyyar mai mulki na daf da karewa

Yanzu haka Jam'iyyar APC mai mulki tana cikin wani matsin lamba game da shirya babban taron ta da ya kamata ace tayi tun ba yau ba amma abin ya faskara har yau.

An hurowa Shugabannin APC wuta su kira babban taro na kasa

Shugaban Jam'iyyar APC John Oyegun

An hurowa Shugabannin Jam'iyyar wuta su shirya babban taro na kasa wanda ya dace ayi tun ba yau ba. Kwanan nan aka shirya zama tsakanin Gwamnonin Jihohi na Jam'iyyar da kuma Shugabannin Jam'iyyar na APC.

KU KATANTA: Sule Lamido yayi tir da Gwamnatin APC

Jaridar Leadership ce ta rahoto wannan labari inda tace an fara zura idanu domin a ga yadda Jam'iyyar za ta fara shiryawa zabe mai zuwa na 2019. Watakila dai APC ba ta da niyyar wani zama sai a tsakiyar shekarar nan.

A watan Yunin bana ne wa'adin Shugabannin Jam'iyyar zai cika. Dama can an zabi su Cif John Oyegun ne a watan Yuni na 2014. Wasu Gwamnoni za su a zauna domin tattaunawa batutuwan da ke gaban su na zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel