Rikicin makiyaya: Na goyi bayan bayanan Shehu Sani a kan Buhari – In ji wani jigon PDP

Rikicin makiyaya: Na goyi bayan bayanan Shehu Sani a kan Buhari – In ji wani jigon PDP

- Wani jigon PDP ya ce yana bayan bayanan Shehu Sani a kan shugaba Buhari

- Sanata Shehu Sani ya bukaci shugaba Buhari ya ziyarci jihar Binuwai inda aka kashe ‘yan asalin jihar da dama

Wani jigo a babban jam'iyyar adawa ta PDP, Cif Sunny Onuesoke, ya bayyana cewa ya goyi bayan sanarwar da aka ce sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya yi a kan shugaba Muhammadu Buhari game da rikicin manoma da makiyaya wanda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Binuwai.

Shehu Sani ya bukaci shugaba Buhari ya ziyarci jihar Binuwai inda makiyaya suka kashe kimani ‘yan asalin jihar 73. Har ila yau, sanatan ya kuma soki lamirin ziyarar da shugabannin jihar suka kai a fadar shugaban kasa a ranar Talata bayan kashe-kashen da aka yi wa mutanen su.

Onuesoke wanda ya yi magana da manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar Binuwai, ya goyi bayan bayanan sanata Shehu Sani a kan shugaba Buhari saboda bai ziyarci jihar ba don ta'azantar wadanda suka rasa 'yan uwa a kisan gillar.

Rikicin makiyaya: Na goyi bayan bayanan Shehu Sani a kan Buhari – In ji wani jigon PDP

Sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya

KU KARANTA: Rikicin Manoma da Makiyaya: An kafa kwamitin kawo sulhu na zama lafiya, karkashin Faresa Yemi Osinbajo

Idan dai baku manta ba Legit.ng ta ruwaito cewa sanata Shuhu Sani ya bayyana cewa bai kamata a ce dattawan jihar Binuwai ne suka ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ba.Maimakon haka, shugaban ne ya kamata ya ziyarce su don yi musu ta’aziyya a kan rashin da suka yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel