Kotu ta tabbatar da haramta kungiyar IPOB a Najeriya

Kotu ta tabbatar da haramta kungiyar IPOB a Najeriya

Babban kotun tarayya da ke zaune a Abuja a ayu Alhamis, 18 ga watan Junairu, 2018 ta yi watsi da karar kungiyar yan asalin Biyafara wato Indegenous People of Biafra IPOB na bukatan kawar da shari’ar haramta kungiyar da kuma lakabata a matsayin kungiyar yan ta’adda.

Yayinda yake gabatar da shari’a akan karar, shugaban babban kotun, Jastis Abdul Kafarati, ya duba dukkan dalilan da yasa aka haramta kungiyar kuma ya tabbatar da su.

Kotu ta tabbatar da haramta kungiyar IPOB a Najeriya

Kotu ta tabbatar da haramta kungiyar IPOB a Najeriya

Ya yi watsi da karar lauyan kungiyar IPOB, Mr. Ifeanyi Ejiofor, na cewa kasancewan ba’ayi ijistan kungiya a Najeriya ba, rijistan ta a kasashen wajen ya isa a kasa hukunta ta.

KU KARANTA: DPR ta rabar da lita 14, 400 ta man fetur kyauta a Abuja

Alkalin ya jaddada cewa haramta kungiyar ya yi daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya a kan kawar da ta’addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel