Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

- Ma'aikatar ayyuka bata tsinana komai a shekarar 2017 ba

- Kawai ma'aikata na zuwa ofis ne suna amsan albashi

Ministan aiki, wutan lantarki da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce ma’aikatarsa bata samu daman aiwatar aiki ko daya a shekaran 2017 ba.

Fashola ya bayyana hakan ne ranan Laraba yayinda ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa kan ayyuka domin bayanai a kan ayyukan da ma’aikatar ta sa cikin kasafin kudin 2018.

Wani mamban kwamitin, Barnabas Gemade, ya tambayesa meyasa ma’aikatar batayi komai a shekarar 2017 ba, ministan ya ce rashin zantar da kasafin kudin 2017 da wuri ne ya sabbaba.

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Ma’aikatar ayyuka bata aiwatar da aiki ko daya ba a 2017 – Minista Fashola

Fashola yace: “An zantar kasafin kudin 2017 a watan Yuni. Akwai doka da ka’idoji kafin sayen kayayyaki wanda ya kai watan Satumba. Kokarin bin doka, sai watan Agusta aka saki kudi.”

KU KARANTA: Kotu ta yanke wa shugaban ƙungiyar haɗin kan malaman musulunci hukuncin ɗaurin rai da rai

Sai shugaban kwamitin ya tambayesa akan ayyukan 2016 da ba’ayi a shekaran ba, Fashola ya gaza bada amsa amma ya bukaci kwamitin ta bashi lokaci zai kawo cikakken bayani daga baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel