Rundunar soji ta tura jami’anta neman turawan da aka sace a Kaduna

Rundunar soji ta tura jami’anta neman turawan da aka sace a Kaduna

- Rundunar sojin kasa ta tura dakaru neman turawan da aka yi garkuwa da su a Kaduna

- Wasu 'yan bindiga da ba a sani ba suka sace turawan guda hudu kan hanyar Abuja

- 'Yan bindigar sun kashe jami’an 'yan sanda guda biyu da ke ba turawan kariya

Rundunar sojojin Najeriya ta tura wasu jami’anta wajen neman wasu Amurkawa biyu da 'yan kasar Canada biyu da wasu ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suka sace a Kaduna.

Wasu 'yan bindiga da ba a sani ba suka sace 'yan kasashen wajen guda hudu a kan hanyar su zuwa Abuja kusa da kauyen Jere da ke cikin jiha ta Kaduna.

Legit.ng ta fahimci cewa, wadannan 'yan bindigar dai sun yi nasarar sace turawan ne bayan sun kashe jami’an 'yan sandan biyu da ke ba su kariya a tafiyar.

Rundunar soji ta tura jami’anta neman Turawan da aka sace a Kaduna

Rundunar sojin Najeriya

Daga bisani rundunar 'yan sanda reshen jihar Kaduna ta ce ta tura jami’anta a kokarin gano Turawan a raye tare da kama 'yan bindigar da suka sace su.

KU KARANTA: Kwana daya bayan taron sulhu a Ekiti, Makiyaya sun kashe wata mata mai ciki

Wata majiyar rundunar sojin kasar ta ce an tura dakaru na musamman daga Abuja domin taimakawa 'yan sanda gano Turawan.

Har lokacin wannan rahoto babu wani bayani da ya fito daga ofisoshin jekadancin kasashen biyu a Najeriya game da Turawan da aka sace.

Rahoto daga kamfanin dillacin labaran AFP ta bayyana cewa ma'aikatun harkokin wajen kasashen biyu sun samu labarin aukuwar lamarin kuma a yanzu haka suna ganawa da hukumomin Najeriya ta yadda za a kubutar da turawan hudu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel