2019: Fadar Aso Rock ta kara haske kan takarar shugaba Buhari

2019: Fadar Aso Rock ta kara haske kan takarar shugaba Buhari

- Bashir Ahmad ya karyata jaridar Reuters

- Jaridar ta ruwaito Buhari yaana cewa ba tabbas ko zaiyi takara

- Zaben 2019 ya kusa isowa jam'iyyu

2019: Fadar Aso Rock ta kara haske kan takarar shugaba Buhari

2019: Fadar Aso Rock ta kara haske kan takarar shugaba Buhari

Rahoton da jaridar Reuters ta buga na cewa shugaban Najeriya a yau da safe ya ce ba tabbas ko zayyi takara karyane, inji mai agazawa shugaban ta fannin soshiyal midiya Mal Bashir Ahmad, wanda yace shugaban bayyi hirar a rediyo ba.

Jaridar ta zayyano shugabann na cewa wai bai yanke shawara ko zai tsaya takara ba, hasali ma ba lallai ya tsaya din ba, kuma yana jira ne yaji ta bakin 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Alkali ya raba auren su saboda lalacin miji

Bashir Ahmad, a shafinsa na tuwita, ya ce jaridar bata fadi gaskiya ba, kuma shugaban bai yi wadannan kalami ba, inda ya ce in gaskiya ne, ai sai a saki sakon muryar tasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel