Fataucin yara: Gwamnatin Kaduna ta dakatar da dauki reno da karbar yara a jihar

Fataucin yara: Gwamnatin Kaduna ta dakatar da dauki reno da karbar yara a jihar

- Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dakatar da dauki reno da karbar yara a jihar

- Gwamnati ta bayyana cewa ta gano wasu daga cikin gidajen marayu suna fatauci da cin zarafin yara

- Hajiya Hafsat Baba ta ce akwai wani dan kasar Ghana wanda ake zargi da sayen 'ya'ya uku a Zariya daga hannun mutanen

Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da dauki reno da karbar yara saboda zaluncin gidaje marayu a jihar, kwamishinan harkokin mata da ci gaban zamantakewa, Hajiya Hafsat Baba ta sanar da haka.

Baba ta bayyana hakan ne a cikin hirarta da NAN majiyar Legit.ng a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu a Kaduna cewa gwamnati ta gano cewa wasu daga cikin gidajen marayu suna fatauci da cin zarafin yara.

Ta jaddada cewa, dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai gwamnati ta gyara tsarin dauki reno da karbar yara a jihar.

Gwamnatin Kaduna ta dakatar da dauki reno da karbar yara a jihar

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai

Ta ce, "A lokacin da muka shigo gwamnati, mun gano cewa mutane kawai sun mayar da gidajensu a matsayin gidajen marayu don su sami wadannan yara, amma ba za su ba da su ga masu neman daukin reno ba. "Maimakon haka, suna amfani da su a matsayin kasuwanci don samun kyauta kuma a kan wannan suka dogara don ciyar da 'ya'yansu”.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta ware naira miliyan 200 domin tallafa wa mata a jihar

"Mun kuma gano cewa ana sayar da wadannan yara, saboda muna ganin cewa wannan lamari ne mai matukar muhimmanci wanda tana bukatar hankalin mu”.

“Daga bisani muka rubuta wa gwamnan jihar wasikar neman amincewa don dakatar da dauki reno da karbar yara domin ba mu san inda ake kai yaran ba".

"Za mu nemar wa wadannan yara adalci, kuma wadannnan batutuwa suna gaban kotu", in ji ta.

Kwamishinan ta bayyana cewa a daya daga cikin shari'ar, wanda ya shafi wani dan kasar Ghana wanda ake zargi da sayen 'ya'ya uku a Zariya wanda ya kai karar ma'aikatar kotu bayan da ta kwace 'ya'yan hannun sa.

“Akwai wani dan kasar Ghana wanda ake zargi da sayen 'ya'ya uku a Zariya, mun tattara wadannan yara daga gare shi, amma ya kai mu gaban kotu kuma a yanzu haka muna kotu a kan maganar. An zargi wannan mutumin da sayen wani yaro N400, 000 da kuma wata yarinya N500,000”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel