Yanzu-Yanzu: Majalisar wakillai ta zartar da wani muhimmin kudurin doka

Yanzu-Yanzu: Majalisar wakillai ta zartar da wani muhimmin kudurin doka

Daga karshe dai majalisar wakillan Najeriya a jiya ta zartar da kudurin dokar nan da aka dade ana tsammani na bangaren harkokin man fetur watau Petroleum Industry Governance Bill, PIGB a turance.

Wannan dai ya na nuni kenan da cewa yanzu za'a yi wa bangaren na harkallar mai a matakin gwamnatin tarayya garambawul da kuma ake sa ran zai kawo sauye-sauye masu ma'ana da dama.

Yanzu-Yanzu: Majalisar wakillai ta zartar da wani muhimmin kudurin doka

Yanzu-Yanzu: Majalisar wakillai ta zartar da wani muhimmin kudurin doka

Legit.ng dai ta samu cewa kudurin dokar dai ya kai shekaru 13 a majalisar tarayyar kafin a samu a zartar da shi biyo bayan tarnaki da kuma cikas da yake samu daga bangarori daban daban na kasar.

A wani labarin mun samu cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jan hankali ga al'ummar kasar nan ta Najeriya da su guji dukkan abun da zai jawo tashin hankali a zabukan shekarar 2019 mai zuwa.

Haka zalika shugaban kasar ta Najeriya ya bayyana cewa hakika tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya taka rawar gani musamman ma wajen ganin ya gabatar da sahihin zaben sannan kuma ya mika mulki yayin da sakamakon ya fita.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel