Tashin hankali: Cutar masassarar Lassa ta bulla a arewa, mutum 3 sun kamu

Tashin hankali: Cutar masassarar Lassa ta bulla a arewa, mutum 3 sun kamu

Shugaban babbar asibitin tarayya dake a garin Keffi na jihar Nasarawa mai suna Dakta Giyan Joshua Ndom ya tabbatar da cewa asibitin sa na kan binciken wasu marasa lafiya su uku da ake zargin sun kamu da cutar nan ta masassar Lassa.

Dakta Joshua yayi wannan kalamin ne yau Alhamis a garin na Keffi yayin da yake zantawa da manema labarai game da lamarin.

Tashin hankali: Cutar masassarar Lassa ta bulla a arewa, mutum 3 sun kamu

Tashin hankali: Cutar masassarar Lassa ta bulla a arewa, mutum 3 sun kamu

Legit.ng ta samu cewa haka zalika hukumar asibitin tuni har ta kebe wadanda ake zargin sannan ta kuma aike da jinin su zuwa a dakunan gwaji domin tabbatar da lafiyar mutanen.

A wani labarin dai mun samu cewa Gwamnan jihar Kogi dake a arewa ta tsakiyar Najeriya mai suna Yahaya Bello ya amince da nadin sabbin Sakatarorin din din din har guda ashirin da daya a ma'aikatu da hukumomin jihar.

Babban sakatariyar ofishin Gwamnan ce dai mai suna Petra Akinti Onyegbule ta sanar da hakan a garin Lokoja babban birnin jihar inda ta kuma bayyana cewa hakan ya biyo bayan garambawul din da gwamnan ke yi a bangaren aikin gwamnatin jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel