Inda ranka! Wata marar hannuwa ta zama matukiyar jirgin sama (Hotuna)
Wata mata da ake kira da suna Jessica Cox da aka haifa ba tare da hannuwa ba a jihar Arizona, kasar Amurka ta jefa dukkan duniya cikin al'ajabi bayan da ta kammala karatun ta na tukin jirgin sama.
Matar mai shekaru 35 a duniya dai majiyar mu ta samu cewa itace mace ta farko da ta taba samun wannan horon a duniya.
Legit.ng dai ta samu cewa matar ta yi karatun koyon tukin jirgin ne dai duk a kasar ta Amurka har na tsawon shekaru uku a duniya sannan kuma tuni har ta fara lashe kyaututtuka kan hakan.
Wannan dai wani karin tabbaci ne ga maganar nan da Hausawa ke fada na cewa babu nakasashe sai kasasshe.
A wani labarin kuma, Shugaban hukumar nan dake ke kula da fasahar kere-kere da zanen taswirar ababen hawa ta gwamnatin tarayyar Najeriya watau National Automotive Design and Development Council (NADDC) a turance watau Jelani Aliyu ya kai wata muhimmiyar ziyara.
Shugaban dai ya kai ziyarar ne yau Alhamis 17 ga watan Janairun shekara ta 2018 zuwa ga wani babban kamfanin kera sassan karfe na motoci mai suna Gorgeous Metal Industries Limited dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng