Buhari ya lashi takobin ladabtar da duk masu shirin tayar da zauni tsaye a 2019

Buhari ya lashi takobin ladabtar da duk masu shirin tayar da zauni tsaye a 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dau alwashin gwamnatinsa ba zata zura idanu tana kallon wasu yan yan tsirarun jama’a su tayar da hankalin yan Najeriya a zabukan 2019 ba.

Buhari ya bada tabbacin gwamnatinsa zata hukunta duk wani wanda ya nemi ya ja da ikon gwamnati na tabbatar da daidaito da kuma kwanciyar hankalin yan Najeriya, musamman na samar da ingantaccen zabuka a 2019.

KU KARANTA: Wutar lantarki ta aika da wani mutumi lahira yayin da yake kokarin satar wayoyin lantarki

Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa a yayin taron tattaunawa da hukumar gidan jaridar Daily Trust suka shirya, inda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda yace yana shawartar yan siyasa dasu ja kunnen magoya bayansu.

Buhari ya lashi takobin ladabtar da duk masu shirin tayar da zauni tsaye a 2019

Buhari

Daga karshe majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana shawartar duk dan siyasan da sakamakon zabe bai yi masa kyau ba daya ya garzaya Kotu don neman hakkinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel