Yanzu-Yanzu: Gwamnan jihar Kogi yayi sabbin nade-nade har 21

Yanzu-Yanzu: Gwamnan jihar Kogi yayi sabbin nade-nade har 21

Gwamnan jihar Kogi dake a arewa ta tsakiyar Najeriya mai suna Yahaya Bello ya amince da nadin sabbin Sakatarorin din din din har guda ashirin da daya a ma'aikatu da hukumomin jihar.

Babban sakatariyar ofishin Gwamnan ce dai mai suna Petra Akinti Onyegbule ta sanar da hakan a garin Lokoja babban birnin jihar inda ta kuma bayyana cewa hakan ya biyo bayan garambawul din da gwamnan ke yi a bangaren aikin gwamnatin jihar.

Yanzu-Yanzu: Gwamnan jihar Kogi yayi sabbin nade-nade har 21

Yanzu-Yanzu: Gwamnan jihar Kogi yayi sabbin nade-nade har 21

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Sakatariyar ta kuma bayyana a cikin takardar manema labaran cewa an zabi sabbin Sakatarorin din-din-din din ne bayan kammala tacewa da kuma tantance su baki daya.

Wadanda aka nada din sun hada da Mr Musa Yahaya Omoyi, Mrs Alfa Ruth Alolo, Mr Igata Boniface Ugwoke, Mr Mohammed Seria Oyenihi, Mr Odei Adinoyi Johnson, Dr. Eje Celestine Ukubile, Mr Negudu Arome Steve, Mr Akpama Paul Sylvanus, Mr Akowe Abimaje Awana, Mr Usman Dan Victor, da kuma Mr Shehu Abdullahi.

Sauran sun hada da Mrs Odiyo Hannah Onyinoyi, Mr Jimoh Adinoyi Mohammed, Mr Idenyi Emmanuel Samson, Mr Idakwoje Labaran Idris, Mr Momoh Abdulkadir Angulu, Mr Alonge Ayo Daniel, Mr Okeme Jibril Abdullahi, Mr Stephen Ojo Peter, Mr Ikuborue Olutoyin Davies da kuma Mr Aina Eric Dele.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel