Tsagerun Neja-Delta sun sha alwashin sake dagulawa shugaba Buhari lissafi

Tsagerun Neja-Delta sun sha alwashin sake dagulawa shugaba Buhari lissafi

Bayan kimanin shekara daya da aka yi na tsagaita wuta a yankin Neja Delta sakamakon yarjejeniyar sulhu da aka shiga tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da kuma tsagerun nan na Neja Delta, za'a sake komawa ruwa.

Alamun hakan dai sun fara bayyana ne bayan da fitattun tsagerun nan na Neja Delta dake tu'annati ga harkokin haka, safara da kuma sayar da mai watau Niger Delta Avengers a turance suka fitar da sanarwar gargadi ga gwamanatin tarayyar.

Tsagerun Neja-Delta sun sha alwashin sake dagulawa shugaba Buhari lissafi

Tsagerun Neja-Delta sun sha alwashin sake dagulawa shugaba Buhari lissafi

Legit.ng ta samu dai cewa tsagerun sun fitar da sanarwar ne a jiya Laraba inda suka sha alwashin dawowa da ayyukan ta'addancin su ga bututan man kasar nan idan har gwamnatinin bata biya masu bukatun su ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a shekarar 2016 da ta gabata dai kungiyar ta Niger Delta Avengers ta kusa durkusar da gwamnatin tarayyar sadda suka bazama suna fasa bututan man kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel