Jam'iyyar adawa ta bukaci kayyade wa'adin mulkin 'yan majalisar Najeriya

Jam'iyyar adawa ta bukaci kayyade wa'adin mulkin 'yan majalisar Najeriya

Yayin da zaben shekara ta 2019 mai zuwa ke ta karatowa, wata jam'iyyar adawa a kasar mai suna Democratic People’s Congress (DPC) a takaice ta bukaci da ayi garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999.

A cewar shugaban jam'iyyar na kasa mai suna Rabaren olusegun Peters, ya kamata a sanya iyaka tare da kayyade wa'adin irin zaman da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke yi a zauren majalisar kamar dai gwamnoni da shugabannin kasa.

Jam'iyyar adawa ta bukaci kayyade wa'adin mulkin 'yan majalisar Najeriya

Jam'iyyar adawa ta bukaci kayyade wa'adin mulkin 'yan majalisar Najeriya

Legit.ng ta samu cewa shi dai shugaban ya bayyana cewa hakan ne kawai mafita ga kasar musamman ma ganin yadda wasu tsiraru ke neman maida majalisar gidan su inda tun da suka je har yanzu basu sauka ba.

A wani labarin dai mun samu cewa Shugaban babbar asibitin tarayya dake a garin Keffi na jihar Nasarawa mai suna Dakta Giyan Joshua Ndom ya tabbatar da cewa asibitin sa na kan binciken wasu marasa lafiya su uku da ake zargin sun kamu da cutar nan ta masassar Lassa.

Dakta Joshua yayi wannan kalamin ne yau Alhamis a garin na Keffi yayin da yake zantawa da manema labarai game da lamarin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel