2019: Kudu maso gabas na Buhari ne – In ji wani jigon APC a kudu

2019: Kudu maso gabas na Buhari ne – In ji wani jigon APC a kudu

Wani jigon jam'iyya mai mulki ta APC a yankin kudu maso gabashin kasar ya ce shaka babu shugaba Muhammadu Buhari zai yi gaggarumin nasara a zaben shekarar 2019 a yankin.

Wani jigon jam'iyya mai mulki ta APC a yankin kudu maso gabashin kasar, kuma babban magoya bayan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, Prince Chemberline Adiaso, ya bayyana cewa shugaban zai yi gaggarumin nasara a zaben shekarar 2019 a yankin.

Adiaso, wanda ya sanar da niyyarsa na takarar gwamna jihar Abiya, ya ce, mutanen yankin kudu maso gabashin sun yanke shawara su bi da kuma goyon bayan shugaba Buhari saboda gaskiyarsa da tsarin jagoranci na gari.

Da yake magana da manema labarai a birnin Abuja ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, Adiaso wanda yake jagorantar magoyan shugaba Muhammadu Buhari a kasashen waje ya ce shugaban ya bayyana a fili cewa yana kaunar ‘yan kabilar Igbo idan aka yi lahakari da irin babbar gagarumin ayyukan ci gaba da ake gudanar a yankin kudu maso gabas tun lokacin da ya shiga ofis.

2019: Kudu maso gabas na Buhari ne – In ji wani jigon APC a kudu

Shugaba Muhammadu Buhari

Legit.ng ta tattaro cewa, Adiaso ya ce yakin neman zaben shugaban kasa Buhari ya fara gadan gadan kuma suna samun goyon bayan mutane.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP na shirin yakar APC ta yanar gizo

Ya kara da cewa manyan shugabannin yankin irin su tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, Gwamnan Imo, Rochas Okorocha; Ken Nnamani; tsohon gwamnan jihar Enugu, Sullivan Chime da wasu manyan shugabannin Igbo suna aiki kuma ba zai tsaya ba don tabbatar da nasara ga APC a kudu maso gabas.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel