Wasu haramtattun tankokin makamashin gas sun shiga hannun hukumar EFCC

Wasu haramtattun tankokin makamashin gas sun shiga hannun hukumar EFCC

A ranar talatar da ta gabata ne, wadansu haramtattun masu dakon mai tare da tankokinsu sun shiga hannun hukumar EFCC reshen birnin Uyo na jihar Akwa Ibom domin gudanar da binciken diddigi tare da gurfanar da su.

Rundunar dakarun sojin ƙasa ta yankin, suke da alhakin damƙo wannan tankoki maƙire da makamashin gas wato Diesel.

Wasu haramtattun tankokin makamashin gas sun shiga hannun hukumar EFCC

Wasu haramtattun tankokin makamashin gas sun shiga hannun hukumar EFCC

Wasu haramtattun tankokin makamashin gas sun shiga hannun hukumar EFCC

Wasu haramtattun tankokin makamashin gas sun shiga hannun hukumar EFCC

Hukumar EFCC ta bayyana cewa, tankokin masu lambobin AKP 222 XA; BNS 298 XA da kuma AKP 224 XA suna dauke da sama da lita dubu talatin da uku ta makamashin gas ba tare da takardun shaidar inda zasu sauke shi ba.

KARANTA KUMA: Osinbajo da gwamnonin jihohi 36 na ganawa a kan tattalin arziki

A yayin damƙar wadannan miyagu, direbobi biyu sun ari ƙafar kare, inda daya daga cikin su, Bello Ibrahim ya shiga hannu tare da karen motarsa, Babangida Adamu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel