Shugaba Buhari zai tika ka da kasa; Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fadawa Sule Lamido

Shugaba Buhari zai tika ka da kasa; Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fadawa Sule Lamido

- Shugaba Buhari yace zai ba Sule Lamido kashi a zabe mai zuwa

- Sakataren Gwamnatin yace Tsohon Gwamnan ba zai kai labari ba

- Lamido yana shirin tsayawa takarar Shugaban kasa a PDP a 2019

Dazu Shugaba Buhari yake cewa zai tika tsohon Gwamnan PDP kuma ‘dan takarar Shugaban Kasa Alhaji Sule Lamido da kasa idan aka fito zaben 2019 a wajen wani taron Jaridar Daily Trust.

Shugaba Buhari zai tika ka da kasa; Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fadawa Sule Lamido

Sakataren Gwamnatin Tarayya tare da Shugaba Buhari

Sakataren Gwamnatin Tarayya ya nuna alamun cewa Shugaba Buhari zai yi takara a 2019. Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustafa wanda ya wakilci Shugaban kasar a taron ya fadawa Lamido wannan dazu nan.

KU KARANTA: Sule Lamido yayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaba Buhari

Boss Mustafa yayi jawabi ne a madadin Shugaban kasar inda ya fara yabawa kokarin ‘Yan kasar a kan siyasar 2015. Kun ji cewa tsohon Gwamnan na Jigawa Sule Lamido ya caccaki Gwamnatin APC mai mulki a taron.

Boss ya maidawa Sule martani inda yace ya duba manufofin sa na takarar sa kuma idan har hakan shi ne kudirin sa to ya shirya shan kashi a hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa a kasar na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel