Hukumar DPR ta rabar da lita 14, 400 ta man fetur kyauta a Abuja

Hukumar DPR ta rabar da lita 14, 400 ta man fetur kyauta a Abuja

A ranar larabar da ta gabata ne, hukumar DPR ta rabar da lita 14, 400 ta man fetur kyauta ga mabukata masu ababen hawa a wani gidan sayar da mai dake kan hanyar Gwagwa-Deidei a Abuja.

An rabar da man fetur din kyauta ga al'umma a sakamakon gidan man dake sayarwa a farashin da ya haura ƙayyadewar gwamnati, kuma ba tare da samun lasisin hukumar ta DPR ba.

A yayin da hukumar ta ke kai komo a jihar domin cafko miyagun gidajen sayar da mai, shugaban hukumar reshen birnin tarayya, Abba Misau, ya kuma bayar da umarnin damƙar mai gidan man, Danladi Eya.

Hukumar DPR ta rabar man fetur kyauta a Abuja

Hukumar DPR ta rabar man fetur kyauta a Abuja

Misau a yayin ganawa da manema labarai ya bayyana cewa, hukumar ta aikata hakan a sakamakon gidan man da yake gudanar da harkokin kasuwanci ba bisa ƙa'ida ba.

KARANTA KUMA: Badaƙalar N92m: Hukumar EFCC ta cafke ɗan tsohon gwamnan jihar Nasarawa

Ya kuma ƙalubalanci dawowar ƙaranci da wahalar man fetur a Abuja a sanadiyar rashin wadatuwarsa a cikin garin da kewaye, inda yace zasu danƙa komai a hannun jami'an tsaro na hukumar NSCDC domin bankaɗo masu janyo tagayyara akan al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel