Tsofaffin mayakan Boko Haram 95 sun dawo cikin al’umman Najeriya – Hedkwatan tsaro

Tsofaffin mayakan Boko Haram 95 sun dawo cikin al’umman Najeriya – Hedkwatan tsaro

- Ba da karfi kawai rundanar sojin Najeriya ke amfani da shi wajen magance kungiyar yan ta’addan Boko Haram ba

- Rundunan ta kafa shiri don ba wadanda suka tuba daga ta’addanci damar zama masu amfani a kasar

- Shirin sake sada tsofaffin yan ta’addan da al’umma ya kasance daya daga cikin muhimman burukan rundunar

An gudanar da wani taro na masu ruwa da tsaki kan sake hada tsoffin mayakan kungiyar Boko Haram da al’umma a yau, Alhamis, 18 ga watan Janairu a hedikwatar tsaro dake Abuja.

An kafa shirin mai taken Operation Safe Corridor ne don samar ma tsofaffin mayakan Boko Haram damar canjawa daga akidarsu, sabuntawa da kuma hadasu da al’umma don taimakawa wajen mayar da rayuwarsu kamar yadda yake a baya.

Tsofaffin mayakan Boko Haram 95 sun dawo cikin al’umman Najeriya – Hedkwatan tsaro

Tsofaffin mayakan Boko Haram 95 sun dawo cikin al’umman Najeriya – Hedkwatan tsaro

Legit.ng ta tattaro cewa a watan Yuli 2017, tsofaffin mayakan Boko Haram 95 aka shigar sansanin don tilasta su ga shirin na makonni 16 wanda ya hada da ilimin likitanci, ilimin zamantakewa, ilimin-ruhaniya ilimin gwaninta har taimakawa wajen amfani da kwayoyi, ilimin boko daga tushe da wasanni.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP na shirin yakar APC ta yanar gizo

An kuma koyar da su sana’o’i tare da taimakon masu gudanarwa daga hukumar daukar ma’aikata.

Tsofaffin mayakan Boko Haram 95 sun dawo cikin al’umman Najeriya – Hedkwatan tsaro

Tsofaffin mayakan Boko Haram 95 sun dawo cikin al’umman Najeriya – Hedkwatan tsaro

Sunyi nasarar kammala shirin kuma lokaci ya yi da za a mika su ga hukumomin jihohinsu domin hada su da al’umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel