An yabi wani dan Najeriya da ya mayar da miliyan N150 da aka tura asusun sa bisa kuskure

An yabi wani dan Najeriya da ya mayar da miliyan N150 da aka tura asusun sa bisa kuskure

- Wani dan Najeriya mazaunin kasar Qatar ya mayar da kudin da aka tura asusunsa bisa kuskure

- Mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin kasashen ketare ta karrama shi

- An bukaci 'yan Najeriya dake zaune a kasashen ketare su zama masu kyawun hali

Mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin kasashen ketare, Honarabul Abike Dabiri-Erewa, ta karrama wani dan Najeriya, Michael Jonathan Asemota, bayan da ya mayar kudi har naira miliyan N150 da aka tura asusunsa bisa kuskure.

Michael Asemota, dan asalin jihar Edo, ya bude asusun ajiya da wani banki a Doha, babban birnin Qatar da adadin kudin kasar QR150,200.

An yabi wani dan Najeriya da ya mayar da miliyan N150 da aka tura asusun sa bisa kuskure

An yabi wani dan Najeriya da ya mayar da miliyan N150 da aka tura asusun sa bisa kuskure

KU KARANTA: Badakalar kudin Makamai: An kara gurfanar da wani jigo a gwamnatin Jonathan

Da yake labartawa Debiri yadda abin ya faru, Asemota, ya ce "Bayan na bude asusun ajiyar na dawo gida, saina samu sako daga banki cewar an saka kudi QR1,502,000 sabanin QR 150,200 da na bude asusun da su. Hakan ya saka na koma bankin na sanar da manajan kuskuren da suka yi, nan take ya mike ya bani hannu muka gaisa bayan ya tabbatar da tafka kuskuren."

Da yake amsa tambayar dalilin da ya saka shi sanar da bankin kuskuren da suka yi, Asemota, ya ce "Na san kudin ba nawa ba ne, kuma sun shiga asusu na ne bisa kuskure, a saboda haka bani da dalilin barinsu a cikin asusun nawa."

Asemota ya shawarci duk wanda ya samu irin wannan matsala da ya gaggauta sanar da bankinsa domin komai dadewa zasu gano inda suka yi kuskure kuma zasu janye kudinsu.

Ya kara da cewa abinda ya yi ya jawowa 'yan Najeriya mazauna Qatar karuwar mutunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel