APC : Kudirin kara wa’adin kwamitin aikace-aikace (NWC) ya raba kawunan gwamnoni APC da kwamitin

APC : Kudirin kara wa’adin kwamitin aikace-aikace (NWC) ya raba kawunan gwamnoni APC da kwamitin

- Jam'iyyar APC ta daga taron da ta shirya da gwamnonin ta a ranar Laraba

- Ana zargi kungiyar gwamnonin APC sun ki halarta taron ne saboda sun samu labarin kudirin kara wa’adin mambobin kwamitin aikace-aikace (NWC)

Rikcin siyasa yana kokarin barkewa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayin da aka daga taro tsakanin gwamnonin APC da mambobin kwamitin aikace-aikace (NWC) a ranar Laraba.

Mai magana da yawun bakin jamiyyar APC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya tabbatar da daga taron, wanda ake sa ran za su tattauna akan shirye-shiryen babban taron da jam’iyyar zata gudanar.

Abudllahi yace shima ta wasikar waya aka sanar dashi an daga taron kuma ba a fada musu dalilin yasa aka daga taron ba, amma za su kira taro a makon dake zuwa

APC Kudirin kara wa’adin kwamitin aikace-aikace (NWC) ya raba kawunan gwamnoni APC da kwamitin

APC Kudirin kara wa’adin kwamitin aikace-aikace (NWC) ya raba kawunan gwamnoni APC da kwamitin

Mataimakiyar gwamnan jihar Osun, Grace Titi Laoye-Tomori, wanda ta wakilci gwamnan jihar Osun, Rauf Aragbesola, ta bayyana fushin ta akan rashin fada mata an daga taron da wuri sai da ta shiga headkwatan APC ta sani.

KU KARANTA : Ba wanda zai shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Sakon PDP zuwa ga gwamnonin APC

Legit.ng ta samu labari cewa, an daga taron ne saboda gwamnonin APC sun ki nuna goyon baya akan yunkurin kara wa’adin mambobin kwamitin aikace-aikace na jam’iyyar.

Wani majiya mai karfi ya fadawa manema labaru cewa, kungiyar gwamnonin APC sun ki halarta taron ne saboda sun samu labarin kudirin kara wa’adin kwamitin aikace-aikace (NWC) najam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel