Osinbajo da gwamnonin jihohi 36 na ganawa a kan tattalin arziki

Osinbajo da gwamnonin jihohi 36 na ganawa a kan tattalin arziki

- Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar tattalin arziki na farko a shekarar 2018.

- An gudanar da wannan taro ne a fadar shugaban kasa

- Taron ya kunshi gwamnoni jihohin Najeriya

A halin yanzu, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yana jagorantar zaman majalisa ta tattalin arziki na farko a wannan sabuwar shekara ta 2018.

Rahotanni da sanadin jaridar The Punch sun bayyana cewa, an fara gudanar da wannan taro ne da misalin karfe 12:15 na ranar yau Alhamis a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo

Legit.ng ta fahimci cewa, majalisar ta kunshi mataimakin shugaban kasar a matsayinsa na shugabanta da kuma gwamnonin jihohi 36 na kasar nan.

KARANTA KUMA: Wata kotu ta gurfanar da mutane biyu da laifin zambar N15m a birnin tarayya

Sauran wadanda ke halartar taron sun hadar da shugaban babban bankin kasa, ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, tare da ministan birnin tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel