Filayen jihar Kogi ba mallakar ka bane: Wani Shugaban al'umma ya gargadi Gwamna Bello

Filayen jihar Kogi ba mallakar ka bane: Wani Shugaban al'umma ya gargadi Gwamna Bello

- Wani shugaban al'umma a jihar Kogi, Yarima Alhassan Ejike yayi kira ga Gwamna Bello ya yi watsi da batun bawa makiyaya filaye a jihar

- Ejike ya ce filayen jihar mallakin al'umma ne saboda haka Gwamnan bashi da ikon dauka ya baiwa baki

- Ejike kuma ya gargadi Gwamna Bello kan fituntunin da ka iya biyo baya idan ya gayyato makiyaya zuwa jihar ta Kogi

Wani shugaban al'umma a jihar Kogi, Yarima Alhassan Ejike ya gargadi Gwamna Yahaya Bello da kar ya kuskura ya fara kafa filayen kiwon shanu a jihar ta Kogi. Ejike ya yi wannan gargadin ne ranar Alhamis yayin da yake hira da manema labarai a Lokoja.

Makiyaya: Wani yariman jihar Kogi ya gargadi gwamna Bello, "Ba kai ke mallakin jihar Kogi ba"

Makiyaya: Wani yariman jihar Kogi ya gargadi gwamna Bello, "Ba kai ke mallakin jihar Kogi ba"

Ejike ya mayar da martani ne ga yunkurin Gwamna Bello na aiwatar da kudirin Gwamnatin Tarayyan na ware filayen kiwo domin makiyaya a jihohin kasar nan don magance rikicin makiyaya da manoma.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayyah za ta samar wa mata da matasa 3m ayyukan yi

Ya kara da cewa jihar Kogi da filayen ta ba mallakin Gwamna Bello bane kuma ya shawarci Gwamnan ya bi a sannu domin gujewa barkewar fitina a jihar da ka iya biyo bayan gayyatar da ya ke mika wa makiyayan.

"Ba kai ke da filayen Jihar Kogi ba, saboda haka baka da ikon daukan filayen da ba mallakar ka ba ka bawa baki," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel