Gwamna Mohammed Abubakar ya ziyarci dalibai 'yan jihar Bauchi dake karatu kasar Czech Republic (hotuna)

Gwamna Mohammed Abubakar ya ziyarci dalibai 'yan jihar Bauchi dake karatu kasar Czech Republic (hotuna)

Rahotanni sun kawo cewa farkon makon da ya gabata ne gwamnan jihar Bauchi, Barista M.A Abubakar ya ziyarci kasar Czech Republic.

Gwamnan ya kai ziyarar ne akan aiki inda yayi amfani da damar wajen ziyartan dalibai 'yan asalin jihar Bauchi dake karatu a kasar ta Czech Republic haka zalika su ma daliban suka yi amfani da wannan damar suka kokawa Gwamnan bukatunsu.

Inda suka bayyanawa Gwamna cewa suna fuskantar kalubale sosai yayin da suke kokarin yin biza zuwa kasar. Sannan kuma suna fuskantar matsalar wajen zama, domin biyan kudin gida a kasar abu ne mai wahala.

Gwamna Mohammed Abubakar ya ziyarci dalibai 'yan jihar Bauchi dake karatu kasar Czech Republic (hotuna)

Gwamna Mohammed Abubakar ya ziyarci dalibai 'yan jihar Bauchi dake karatu kasar Czech Republic

Bayan gwamna ya saurari koke daliban, ya sha alwashin cewa da yardar Allah wadannan nasu sun zo karshe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: A yau Buhari zai karbi sabbin Jakadai guda 3 daga kasashen waje

Sannan gwamnan ya bayyanawa daliban cewa Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin jagorancinsa tana shirye da ta ba su duk wata gudummawar da ta dace dan inganta musu karatunsu da saukaka musu dawainiyar karatu.

Gwamna Mohammed Abubakar ya ziyarci dalibai 'yan jihar Bauchi dake karatu kasar Czech Republic (hotuna)

Gwamna Mohammed Abubakar ya ziyarci dalibai 'yan jihar Bauchi dake karatu kasar Czech Republic

Daga bisani bayan Gwamnan ya kammala da daliban, sai ya ziyarci ofishin ma'aikatar cikin gida na kasar domin tattauna yadda za a sama musu mafita dangane da matalolin da suke fiskanta a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel