Tsoron barkewar cutar LASSA fever ya sa an rufe wasu makarantu

Tsoron barkewar cutar LASSA fever ya sa an rufe wasu makarantu

- Lassa Fever cutar zazzabi ce da beraye ke yadawa

- Ana samun bullar cutar akai-akai a sassan Najeriya

- Tana da matukar hadari da kisan farat daya

Tsoron barkewar cutar LASSA fever ya sa an rufe wasu makarantu

Tsoron barkewar cutar LASSA fever ya sa an rufe wasu makarantu

A ranar alhamis dinnan gwamnatin Ebonyi ta umarci a rufe dukkanin makarantu na jihar domin daukan mataki akan cutar lassa wanda ya faru a jihar kwanan nan.

Kwamishinan Ilimi na jihar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a wata hira da yayi a Abakaliki, inda yake cewa rufewan wata hanya ce na daukan matakan suka dace game da cutar. A cewar sa, gwamnatin tana kokarin ganin ta dauki matakin gaggawa domin ganin tsayar da cutar wanda tayi sanadiyyar rayuka ciki har da likitoci guda biyu. Ya kara da cewar cutar bata yadu da yawa ba, amma rufe makarantun zai taimaka wurin hana yaduwar cutar.

Kwamishinnan ya kara da cewar daya daga cikin hanyoyin da za'a bi wurin ganin an magance cutar shine rufe makarantun har sai an tabbatar da cewar cutar bata shafi dalibanmu ba.

Har ila yau, cibiyar binciken lafiya NOFIC ta Abakaliki sun kwashe majinyata daga asibitin tarayya na Abakaliki saboda barkewan cutar.

DUBA WANNAN: Bulala shida kadai ga mazajen da suka yi fade

Majalisar dokokin jihar ta kira ga masu kwangilar da suka gina cibiyar a ranar larabar nan da su bayyana a gabanta, akan cewar basu cika ka’idar da aka basu ba.

Kakakin Kungiyar ta NOFIC, Rita Nwojiji, ta tabbatar da fitar da marasa lafiyan. A cewar ta fitar da marasa lafiyan zai taimaka wa asibitin wurin magance cutar, domin tabbatar da cutar bata shafi wanda basu kamu da ita ba. Ta tabbatar da cewa zuwa ranar litinin ana sa ka ran za a sake dawowa aiki

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel