Gwamnatin Taraba ta ba da umurnin kama wadanda suka kashe dan majalisa

Gwamnatin Taraba ta ba da umurnin kama wadanda suka kashe dan majalisa

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya umurci jami’an tsaro a jihar da su tsamo wadanda suka kashe dan majalisa mai wakiltanmazabar Takum 1, a majalisar dokokin jihar Taraba, mai girma Hosae Ibi.

Gwamnan ya bayyana rokon ne a lokacin da mambobin majalisar jihar Taraba suka ziyarce shi a gidan gwamnati dake Jalingo, babban birnin jihar.

Yan majalisan, karkashin jagorancin kakakin majalisar, mai girma Peter Abel, sun kasance a gidan gwamnatin ne don jajentawa gwamna Ishaku bisa kisan rashin imani da aka yiwa dan’uwansu wanda ya kasance daga karamar hukuma daya da gwamnan jihar.

Yayinda yake magana a madadin tawagar, mai girma Abel ya bayyana rashin jin dadi akan labarin kisan mai girma Ibi.

Ya zargi masu laifin tare da niyyar kashe shi ba tare da wata manufa ba.

Gwamnatin Taraba ta ba da umurnin kama wadanda suka kashe dan majalisa

Gwamnatin Taraba ta ba da umurnin kama wadanda suka kashe dan majalisa

Duk da haka, yayi kira ga mutane da su ajiye banbancin siyasa a gefe su kuma tabbatar da cewan masu laifin basu samu zaman lafiya ba a jihar.

Yayinda yake bayyana ra’ayinsa, gwamna Ishaku ya ce bai ji dadin lamarin ba, musamman tare da dukkan kokari da aka karfafa don ganin an sako shi.

Gwamnan wanda bai iya boye bakin cikinsa ba yayi korafi akan matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta da kuma kiran gaggawa ga wajen kawo karshen hakan.

Yayinda yake yabawa kokarin hukumomin tsaro a jihar, gwamna Ishaku ya bukacesu da su tabbatar da cewa an gano masu hannu a kisan.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP na shirin yakar APC ta yanar gizo

Gwamnan ya cigaba da shawartan mutane da su kasance masu kula su kuma kai rahoton fuskokin mutane da basu da masaniya akansu ga hukumomin tsaro.

Yayi kira ga mutanen jihar da kada su dauki mataki a hannunsu kamar yanda zaku dauki abinda ya faru a matsayin laifi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel