Mutane 2 ne suka rasu ba 5 ba kamar yadda Gwamna Ortom ya ce, inji Jimoh Moshood

Mutane 2 ne suka rasu ba 5 ba kamar yadda Gwamna Ortom ya ce, inji Jimoh Moshood

- Kakakin Rundunar Yan sanda, Jimoh Moshood ya ce rundunar tayi nasarar kwantar da tarzomar da ta taso a Benuwe sai dai abin da ba'a rasa ba

- Moshood kuma ya ce gawar mutane biyu ne rundunar ta gano ba biyar ba yadda Gwamna Ortom na Jihar Benuwe ya fadi

- Moshood ya kuma ce rundunar tana cigaba da gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata kisan kuma a hukunta su

Kakakin Rundunar yan Sandan Najeriya, Jimoh Moshood ya ce mutane biyu ne suka mutu a harin da aka kai a jihar ba biyar ba kamar yadda Gwamnan Jihar Benuwe Samuel Ortom ya fadawa shugabanin kudu da suka je masa ta'aziya a ranar Laraba

Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ya yi sharhi kan rikicin jihar Benuwe

Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ya yi sharhi kan rikicin jihar Benuwe

Duk da cewa rundunar yan sandan ta baza Jami'ai sama da 6000 a lunguna da sakunan jihar, an samo rahoton tsintar gawar mutum biyu a jiya wanda har yanzu jami'an tsaro na cigaba da gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata hakan kuma a hukunta su.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayyah za ta samar wa mata da matasa 3m ayyukan yi

Kakakin rundunar yan sandan Najeriya, Jimoh Moshood a wata hira da yayi ta gidan talabijin na Channels ya ce hukumar tayi nasarar kwantar ta tarzomar sai dai dan abin da ba za a rasa ba. Ya kuma ce ba mutane biyar ne suka rasu ba kamar yadda wasu ke yadawa, mutum biyu ne kawai.

A wani gefen kuma, 'Yan majalisar Dattawa sunyi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara sa ido kan batun tsaro a kasar domin yana daya daga cikin nauyin da ke kansa na farko.

Wasu daga cikin yan majalisar kuma sun ce ba daidai bane a bawa makiyaya filayen kiwo kyauta a jihohi, kamata yayi su saya domin kiwo ma kasuwanci ne kuma gwamnati ba ta bawa sauran yan kasuwa filayen kafa kasuwancin su kyauta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel