Kakakin hukumar 'yan sandan Najeriya ya fadi dalilin da ya hana rikicin makiyaya karewa

Kakakin hukumar 'yan sandan Najeriya ya fadi dalilin da ya hana rikicin makiyaya karewa

- Kakakin hukumar 'yan sandan Najeriya ya fadi abinda ke kara hura wutar rikicin makiyaya

- Ya zargi kalaman wasu batagari daga cikin 'yan siyasa da kara jawo rincabewar rikicin

- Ya ce hukumar 'yan sandan Najeriya na iya bakin kokarinta domin hana yaduwar rikicin

Kakakin hukumar 'yan sandan Najeriya, Jimoh Moshood, ya dora laifin rincabewar rikicin makiyaya da manoma a jihar Benuwe da wasu jihohin Najeriya a kan kalaman wasu batagari daga cikin 'yan siyasa.

Moshood ya bayyana haka ne a wani shirin gidan talabijin na Channels da safiyar yau.

Da yake karin bayani a kan rawar da hukumar 'yan sanda ta taka wajen dakile rigimar makiyaya da manoma a jihar Benuwe, Moshood ya ce "kalaman bangarorin dake rikicin da kuma na wasu 'yan siyasa na kara hura wutar rigingimun da muke kokarin kwantarwa."

Kakakin hukumar 'yan sandan Najeriya ya fadi dalilin da ya hana rikicin makiyaya karewa

Kakakin hukumar 'yan sandan Najeriya; Jimoh Moshood

Kazalika, ya bayyana cewar hukumar 'yan sanda ta aike da gargadi ga masu yin kalaman da kan iya kara jawo rincabewar rikicin tare da tabbatar da shirin hukuma na gurfanar da duk wanda ta samu da laifin aikata hakan.

"Ba iya rikicin kawai zamu kwantar ba, dole mu yi yaki da duk wani abu da kan iya haifar afkuwar hargitsi. Hakan ya hada har da kalamai dake barazana ga zaman lafiyar jama'a," a cewar Moshood.

DUBA WANNAN: Majalisar dattijai za ta gudanar da muhimmin taron kwana biyu sati mai zuwa

Jawabin na Moshood na zuwa ne kwana daya kacal bayan gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom ya tabbatar da sake kai wasu sabbin hare-hare a kananan hukumomin Logo, Guma, da Okpokwu dake jihar.

Gwamna Ortom ya bayyana cewar mata biyu aka kashe a Guma, wasu mutane biyu a Logo ranar Talata, yayin da wasu da aka kashe wasu da dama a karamar hukumar Okpokwu a sabbin hare-haren.

Saidai hukumar 'yan sanda ta ce mutum biyu ne kawai suka mutu yayin harin.

Moshood ya ce "Ba mutum biyar ba ne suka mutu kamar yadda rahotanni ke yadawa ba, hukumar 'yan sanda ta tabbatar da mutuwar wasu mata biyu ne a Guma."

Ya kara da cewar hukumar 'yan sanda ta dauki matakan ganin cewar sabbin hare-hare basu yadu zuwa wasu sassan jihar ba, yana mai bayyana yadda suka samu rahoton kai hari a kan wasu makiyaya a wani yankin jihar Enugu mai makobtaka da jihar Benuwe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel