Tsohuwar kwamishina a jihar Benuwe ta jagoranci masu zanga-zanga a birnin Abuja akan kashe-kashen da makiyaya suke yi

Tsohuwar kwamishina a jihar Benuwe ta jagoranci masu zanga-zanga a birnin Abuja akan kashe-kashen da makiyaya suke yi

- Yan jihar Benuwe sun gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja a ranar Alhamis

- Masu zanga-zanga sunyi kira da gwamnatin tarayya ta dakatar da kashe-kashen da ake yi a jihar Benuwe

Wata tsohuwar kwamishina daga jihar Benuwe ta jagoranci masu zanga- zanga a birnin Abuja akan kashe-kashen da makiyaya suka yi a jihar makonni biyu da suka gabata.

Margaret Iyorembr, tsohuwar kwamishina ma'aikatan harkokin mata na jihar Benuwe ta fadawa Legit.ng ta ce yakamata duniya ta san abun dake faruwa a jihar.

Margaret ta ce inda aka duba gefen ta za a ga babban fosta da aka rubuta, “Makiyaya sun zo garin mu, sun kashe kabilan Tiv wanda ya hada da mata, kana yara, da iyaye mata masu juna biyu".

Tsohuwar kwamishina a jihar Benuwe ta jagoranci masu zanga-zanga a birnin Abuja akan kashe-kashen makiyaya ke yi

Babu wanda ya tsokane su, wannan abu ya dade yana faruwa a jihar Benuwe, lokaci yayi da yakamata duniya ta san ainihin abun dake faruwa a Najeriya.

KU KARANTA : Zai yi matukar wahala Buhari ya sake nasarar zabe a 2019 - Sheikh Gumi

Margaret ta ce ya zama dole gwamnatin tarayya ta hana kashe-kashen da ake yi a jihar Benuwe kuma ta tabbatar da an kama masu laifin da wadanda suke daukan nauyin su.

Kisan kare dangi shine abun dake faruwa jihar Benuwe

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel