Jam’iyyar PDP na shirin yakar APC ta yanar gizo

Jam’iyyar PDP na shirin yakar APC ta yanar gizo

Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Yemi Akinwunmi, ya bukaci matasan jam’iyyar da su yada a shafukan zumunta tare da fallasa rashin nasarorin gwamnatin jami’iyyar APC wanda shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta.

Mataimakin shugaban jam’iyyar ya nuna bukatar hakan ne a taron cudanyan kungiyoyin matasan PDP tare da shugaban matasan kasa na jam’iyyar, mai girma S.K.E Udeh-Okoye a hedikwatar jam’iyyar, ya ce jam’iyyar baza ta wahala ba wajen yakin neman zabe idan matasan suka yi amfani da yanar gizo don yada rashin nasarorin wannan gwamnatin.

Yayinda yake raddi akan ministan wutar lantarki, gidaje da ayyuka, Babatunde Fashola, kan rashin nasarar isar da aikinsa, ya tuno a baya cewa ministan, a lokacinda yake mukamin gwamna ya ce “muhimmiyar gwamnati zata gyara wuta cikin watanni shida."

Ya cigaba da cewa “akalla shekaru uku kenan yanzu, basu yi komai ba. Abubuwa suna cigaba da tabarbarewa kullun.

KU KARANTA KUMA: Matasa sun yi zanga-zanga akan rashin wutar lantarki a jihar Niger

Mataimakin shugaban ya bayyana rashin jin dadinshi akan abunda ya sanyawa batu “zabi” wajen hukunci da rashawa, inda ya fahimci cewa yan PDP kadai gwamnatin Buhari ke hukuntawa.

A jawabi da ya taba yi a baya, mai girma Udeh-Okoye ya bukaci kungiyoyin matasa da su hada hannu tare das hi don sauke jam’iyyar APC a 2019, ya cigaba da cewa sake daura jam’iyyar PDP a mulki ne ya bashi karfin yanke shawarar tsayawa takaran ofishin shugaban matasan kasa na jam’iyyan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel