Kasar Jamus za ta kashe euro miliyan 120 don magance cutar Polio a Najeriya - Elias Fatile

Kasar Jamus za ta kashe euro miliyan 120 don magance cutar Polio a Najeriya - Elias Fatile

- Jamus zata tallafawa Najeriya da miliyoyin kudi dan magance cutar Polio a fadin kasar

- Gwamnatin kasar ta yi yajejeniya da gwamnatin Najeriya akan taimaka mata a fanoni daban- daban

Mai magana da yawun bakin ma’aikatan kula da harkokin kasashen waje, Elias Fatile, ya ce Kasar Jamus za ta kashe euro miliyan 120 don magance cutar Polio a Najeriya.

Elias Fatile ta bayyana haka ne a taron manema labaru da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.

Gwamnatin kasar Jamaus ta yi yarjejeniya da gwamnatin Najeriya akan taimaka mata a fanoni daban- daban a shekara 2016 a ciki har da magance cutar Polio.

Kasar Jamus za ta kashe euro miliyan 120 don magance cutar Polio a Najeriya - Elias Fatile

Kasar Jamus za ta kashe euro miliyan 120 don magance cutar Polio a Najeriya - Elias Fatile

A cikin abubuwan da tayi akawari zata ba Najeriya hadda tallafin euro miliyan 120 don magance cutar Polio a kasar.

KU KARANTA : Shittu ya zargi Ajimobi da nuna bangaranci da raba kawunan yan APC a jihar Oyo a wasikar da ya rubutawa Buhari

Ya kara da cewa, tawaga daga majalissar dokokin kasar Japan sun ziyarci Najeriya don nazarin matakin hadin kai tsakanin Japan da Najeriya, ta hanyar Jakadanci Kasuwanci.

Ministan kula da harkan kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya tarbi tawagar a madadin gwamnatin tarayya inji Elias

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel