Majalisar dattijai za ta gudanar da muhimmin taron kwana biyu sati mai zuwa

Majalisar dattijai za ta gudanar da muhimmin taron kwana biyu sati mai zuwa

- Majalisar dattijai ta bayyana cewar za ta dakatar da zaman majalisa na kwanaki biyu a satin gaba

- Majalisar ta dauki wannan mataki ne domin samun gudanar da wani muhimmin taro a kan batun tsaro

- Sanatan Najeriya Shuaibu Lau ya gabatar da kudirin hakan gaban majalisar

Majalisar dattijai ta yanke shawarar dakatar da zamanta na kwanaki biyu a satin gaba domin gudanar da wani taron kasa a kan batun tsaro. Za'a gudanar da taron ne a ranakun Laraba da Alhamis na satin gaba.

Majasilar ta yanke wannan shawara ne bayan da Sanatan Najeriya mai wakiltar jihar Taraba ta arewa, Shuaibu Lau, ya jawo hankalin mambobin majalisar a kan hare-haren makiyaya a jihar Taraba da wasu jihohin Najeriya.

Majalisar dattijai za ta gudanar da muhimmin taron kwana biyu sati mai zuwa

Majalisar dattijai za ta gudanar da muhimmin taron kwana biyu sati mai zuwa

Tun da farko, mambobin majalisar sun bayyana cewar zasu gudanar da taron kasa domin tattaunawa a kan batun tsaro, saidai basu fadi ranar da zasu yi taron ba har saida Sanata Lau ya gabatar da kudirin.

KU KARANTA: Badakalar kudin Makamai: An kara gurfanar da wani jigo a gwamnatin Jonathan

Wani rahoton mambobin majalisar da suka ziyarci jihar Benuwe ya ce yaduwar kananun makamai ne babban makasudin afkuwar rigingimu tsakanin makiyaya da manoma. Kazalika rahoton ya zargi rashin jami'an tsaro a kauyuka da bawa batagari damar cin karensu babu babbaka.

A shawarwarin da mambobin majalisar suka bayar, sun bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da binciken kwakwaf domin zakulo masu hannu cikin kai hare-haren tare da tabbatar da an gurfanar da su gaban Shari'a.

Hakazalika sun bukaci gwamnati da ta sake nazarin yadda take raba jami'an tsaro domin tabbatar da ba'a bar mazauna kauyuka cikin rashin tsaro ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel