Jihar Ebonyi ta kulle makarantu a kan zazzabin Lassa

Jihar Ebonyi ta kulle makarantu a kan zazzabin Lassa

- Ciwon zazzabin Lassa ya addabi jihar Ebonyi

- Gwamnatin jihar ta bada umarnin kulle dukkan makarantun jihar

Gwamnatin jihar Ebonyi ta kulle dukkan makarantun jihar bisa ga sabuwar yaduwar zazzabin Lassa wanda ya hallaka rayukan ma’aikatan asibiti kuma da daman a kwance a asibitin Irrua specialist hospital.

Kwamishanan ilimin jihar, Farfesa John Eke, wanda yayi wannan sanarwa ga manema labari a Abakalili ya ce an yanke wannan shawara ne bayan wata mata da danta sun sami cutan a jiya.

Jihar Ebonyi ta kulle makarantu a kan zazzabin Lassa

Jihar Ebonyi ta kulle makarantu a kan zazzabin Lassa

Farfesa Eke ya ce domin tabbatar da rayukan yan makaranta a jihar, za’a kulle dukkan makarantu daga yanzu zuwan ranan Juma’a, 26 ga watan Junairu. Kana an gargadi iyaye da su san wadanda yaran ke wasa dasu kuma su tabbatar da tsaftan muhallansu.

KU KARANTA: Zai yi matukar wahala Buhari ya sake nasarar zabe a 2019 - Sheikh Gumi

Yayinda jaridar Leadership ta kai ziyara wasu makarantu masu zaman kansu, an samu cewa ma’aikatan makarantun suna mayar yara gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel