Yanzu Yanzu: A yau Buhari zai karbi sabbin Jakadai guda 3 daga kasashen waje

Yanzu Yanzu: A yau Buhari zai karbi sabbin Jakadai guda 3 daga kasashen waje

- Ana sanya ran jakadu 3 zasu gabatar da wasikun kama aiki ga shugaban kasa Buhari

- Jakadu ne na kasar Greece ga Najeriya, babban kwamishinan Bangladesh da kuma jakadan Portugal

- Fadar shugaban kasa bata sanar da ainahin lokacin da ake sa ran isowarsu ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi sabbin Jakadai daga kasashen waje guda uku a yau Alhamis, 18 ga watan Janairu.

An sanar da ci gaban ne a wani rubutu da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na twitter, @NGRPresident.

KU KARANTA KUMA: Matasa sun yi zanga-zanga akan rashin wutar lantarki a jihar Niger

Legit.ng ta tattaro cewa jakadun da ake sanya ran zasu gabatar da wasikun su sune Ms. Maria Saranto jakadiyar Greece ga Najeriya, H.E. Maj. Gen. Kazi Sharif Kaikoband na Bangladesh, da kuma jakadan Portugal, H.E. Mr. Anthonio Pedro Da Vinha Rodrigues Da Silva.

Ba’a sanar da ainahin lokacin da ake sa ran isowarsu ba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel