Rikicin mai: Sanatoci na zargin juna da hada baki da NNPC

Rikicin mai: Sanatoci na zargin juna da hada baki da NNPC

Yan majalisan dattijai a jiya Laraba sun soki rahoton kwamitin majalisar dattawa a kan man fetur da rashin sanya al’amarin tallafin man fetur a cikin rahoton.

Sanatocin sun ce rahoton sunyi zargin cewa kamfanin NNPC ta yi sake-sake cikin rahoton da kwamitin ta zo gabatarwa majalisa.

Sanatocin sun soki shugaban kwamitin, Sanata Kabir Marafa, a kan rashin sanya zancen tallafin kudin mai wanda sukayi zargin cewa fadar shugaban kasa ta biya ba tare da izini da ilimn majalisan dokoki ba.

Rikicin mai: Sanatoci na zargin juna da hada baki da NNPC

Rikicin mai: Sanatoci na zargin juna da hada baki da NNPC

Daga cikin sanatocin da sukayi magana sune Sanata Stella Oduah wacce ta ce tana bada shawara kawai ayi watsi da rahoton. Kana sanata Godswill Akpabio ya ce wannan rahoto zubar da mutuncin majalisan ne.

KU KARANTA: Martanin Fati Mohammed ga wasikar da wani Malam Datti Assalafiy ya aika mata

A cikin rahoton, Sanata Marafa ya kawo shawarwari guda 5 domin samun mafita daga cikin rikicin man fetur.

Ga dukkan alamu dai, kwamitin majalisar dattawa kan man fetur na kokarin rufa-rufa kan Karin N26 da gwamnati ke bada tallafi kan kowani litan mai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel