Badakalar kudin Makamai: An kara gurfanar da wani jigo a gwamnatin Jonathan

Badakalar kudin Makamai: An kara gurfanar da wani jigo a gwamnatin Jonathan

- EFCC ta fara binciken yadda tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Pius Anyim

- Binciken EFCC ya bayyana yadda Anyim ya karbi miliyan N575 daga cikin kudin makamai

- Anyim ya musanta zargin hukumar EFCC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim, ya shiga tsaka mai wuya bayan hukumar EFCC ta bankado yadda ya karbi wasu kudi har naira miliyan N575 a matsayin kudin aiyuka na musamman daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Sambo Dasuki.

Jami'an hukumar EFCC na binciken gano wanne irin aiyuka na musamman Anyim ya gudanar da kudin, bayan ba shine ministan aiyukan gwamnatin tarayya na musamman ba.

Badakalar kudin Makamai: An kara gurfanar da wani jigo a gwamnatin Jonathan

Badakalar kudin Makamai: An kara gurfanar da wani jigo a gwamnatin Jonathan

Saidai a jawabin da ya yi wa hukumar EFCC, Anyim, ya nesanta kansa da asusun ajiyar aiyuka na musamman, yana mai bayanin cewar ofishin mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro keda alhakin yin hada-hadar kudi ta asusun.

KU KARANTA: Ba mu da filayen kiwon shanu, in ji Gwamnatin Jihar Taraba

Saidai binciken hukumar EFCC ya tabbatar da cewar Anyim ya saka hannun karbar kudi, N500,00,000.00 a ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2015 daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro. Kazalika hukumar ta kara samun wasu bayanai dake nuna Anyim ya kara karbar wasu kudin N20,000,000.00 a ranar 14 ga watan Maris na shekarar 2015 daga ofishin Sambo Dasuki. Sannan EFCC ta ce kafin hakan, Anyim, ya karbi wasu kudin, miliyan N30 a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2013.

EFCC ta kara da cewar, Anyim, ya karbi dukkan wadannan kudade ne da sunan gudanar da wasu aiyuka na musamman da har yanzu ba ta iya tantancewa da su ba.

Hukumar ta ce tana cigaba da binciken Anyim duk da kasancewar an bayar da shi beli.

Anyim dai ya ce sanayya ce kawai irin ta aiki tsakaninsa da Sambo, yana mai bayyana cewar bai san komai a kan kudaden da hukumar EFCC ke tuhumar sa da karba ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel