Sabon salo: An nada Ministan kewa da kadaici a Kasar Ingila

Sabon salo: An nada Ministan kewa da kadaici a Kasar Ingila

- Kasar Ingila ta samu Ministan kadaici a makon nan

- Ministan zai kula da masu fama da kadaici da kewa

- Kwanaki a Jihar Imo an bada shigen wannan mukami

Kasar Ingila ta Turai na shirin kawo karshen masu fama da kadaici a Birtaniya don haka aka nada Ministan da zai yi wannan babban aiki. Akwai mutane da dama da kadaici yayi masu yawa a kasar.

Sabon salo: An nada Ministan kewa da kadaici a Kasar Ingila

Kasar Ingila ta ware Ma'aikata na Makadaita a Birtaniya

Kusan mutane miliyan 9 ne ke fama da kadaici a Ingila inji Hukumar Red Cross ta Duniya don haka Gwamnatin Birtaniya ta kama hanyar shawo kan wannan matsala. Shugabar Kasar Theresa May tace za a kawo karshen wannan takaicin ga Jama’a.

KU KARANTA: Malaman da mu ka kora su na iya neman aiki - Gwamnan Kaduna

Karamin Ministan wasanni na kasar Tracey Crouch ne zai rike wannan Ma’aikata domin fama da kadaici a Kasar. Mutane musamman Dattawa da masu aiki ke fama da irin wannan matsala inda wasu da dama ke boye abin da ke ran su a cikin zukatan su.

Kadaici dai mugun abu ne don haka Firayim Ministar kasar ta ce dole tayi bakin kokarin ta wajen kawo karshen sa. Tuni an gama tsare-tsaren yadda za a magancewa Jama’a kewan su a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel